Ba zamu lamunci matakan ko kin zuwa wurin aiki ba -Shugaban SUBEB
Daga JB Danlami Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha, Malam Yusif Kabir, ya nuna damuwarsa bisa halayyar wasu malaman makaranta ta kin zuwa wuraren aiki. Malam Yusif ya furta haka ne, a ganawarsa da sashen yada labarai na Hukumar. Shugaban Hukumar, ya kara da cewa a dai dai lokacin da Gwamnatin jiha ta futo da managartan tsare- tsare na inganta harkokin ilimi ta hanyar inganta rayuwar malaman musamman ta wajen biyansu albashi a kan lokaci da sanya musu kudin Karin girma, amma wasu malamai marasa kishi sun ci gaba da halayyar kin zuwa wuraren aikinsu na koyarwa. Ya ci gaba da cewa hukumar, ta kara inganta fannin duba makarantu don samun cikakken bayanan abubuwa da suke wakana a makarantun da nufin daukar matakin da ya dace. Don haka ya ja hankalin wadanda suke da irin wannan halayya su sauya tun kafin hukumar ta dauki matakin ladaftarwa a kansu. Malam Yusif ya yi amfani da wannan dama, ya godewa Gwamna injiniya Abba Kabir Yusif bisa bayar da ...