Ba zamu lamunci matakan ko kin zuwa wurin aiki ba -Shugaban SUBEB

Daga JB Danlami 

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha, Malam Yusif Kabir, ya nuna damuwarsa bisa halayyar wasu malaman makaranta ta kin zuwa wuraren aiki.
Malam Yusif ya furta haka ne, a ganawarsa da sashen yada labarai na Hukumar.

Shugaban Hukumar,  ya kara da cewa a dai dai lokacin da Gwamnatin jiha ta futo da managartan tsare- tsare na inganta harkokin ilimi ta hanyar inganta rayuwar  malaman musamman ta wajen biyansu albashi a kan lokaci da  sanya musu kudin Karin girma, amma wasu malamai marasa kishi  sun ci gaba da halayyar kin zuwa wuraren aikinsu na koyarwa.

Ya ci gaba da cewa hukumar, ta kara inganta fannin duba makarantu don samun cikakken bayanan abubuwa da suke wakana a makarantun da nufin daukar matakin da ya dace. Don haka ya ja hankalin wadanda suke da irin wannan halayya su sauya tun kafin hukumar ta dauki matakin ladaftarwa a kansu.

Malam Yusif ya yi amfani da wannan dama, ya godewa Gwamna injiniya Abba Kabir Yusif bisa bayar da fifiko ga fannin ilimi inda ya bukaci allummar jihar nan da su kara bai wa gwamnti goyon baya a kokarinta na inganta harkokin ilimi da sauran al’amura da suka shafi ci gaban jjhar nan.

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!