Posts

Showing posts from June, 2025

HATSARIN MOTA DA YA RUTSA DA MATASA 22 'YAN ASALIN JIHAR KANO: KUNGIYAR ÀoPSHoN TA YI TA'AZIYYA

Daga JB Danlami  An shiga cikin jimami da alhini a jihar Kano bayan wani mummunan hatsarin mota da ya lakume rayukan matasa 22 ‘yan asalin jihar. Wannan hatsari ya rutsa da matasan a lokacin da suke dawo wa gida Kano bayan kammala gasar wasanni ta kasa a birnin Abekutan na Jihar Ogun.   Hatsarin ya faru ya  girgiza al’ummar jihar da ma kasa baki daya, kasancewar ya yi sanadiyyar mutuwar matasa da dama. A wani bangare na nuna alhini da jajantawa, Shugaban Kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare ta Najeriya reshen ÀoPSHoN, Kwamarad Malam Abdussalam Sumaila, ta  hannun Sakatariyar kungiyar, Kwamarad Bilkisu T. Abdulkadir, sun gabatar da sakon ta'aziyya ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da kuma iyalan marigayan  da daukacin al’ummar jihar baki daya. Kwamarad Abdussalam ya bayyana cewa wannan babban rashi ne da zai dade ana tuna shi, musamman ganin cewa wadanda abin ya shafa matasa ne da ak...