HATSARIN MOTA DA YA RUTSA DA MATASA 22 'YAN ASALIN JIHAR KANO: KUNGIYAR ÀoPSHoN TA YI TA'AZIYYA


Daga JB Danlami 

An shiga cikin jimami da alhini a jihar Kano bayan wani mummunan hatsarin mota da ya lakume rayukan matasa 22 ‘yan asalin jihar. Wannan hatsari ya rutsa da matasan a lokacin da suke dawo wa gida Kano bayan kammala gasar wasanni ta kasa a birnin Abekutan na Jihar Ogun.  
Hatsarin ya faru ya  girgiza al’ummar jihar da ma kasa baki daya, kasancewar ya yi sanadiyyar mutuwar matasa da dama.

A wani bangare na nuna alhini da jajantawa, Shugaban Kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare ta Najeriya reshen ÀoPSHoN, Kwamarad Malam Abdussalam Sumaila, ta  hannun Sakatariyar kungiyar, Kwamarad Bilkisu T. Abdulkadir, sun gabatar da sakon ta'aziyya ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da kuma iyalan marigayan  da daukacin al’ummar jihar baki daya.

Kwamarad Abdussalam ya bayyana cewa wannan babban rashi ne da zai dade ana tuna shi, musamman ganin cewa wadanda abin ya shafa matasa ne da ake da kyakkyawan fata a gare su wajen gina jihar da kasar baki daya. Ya kara da cewa, “Dukkanmu ba za mu manta da wannan rana ba, domin asarar rayuka 22 a lokaci guda wani babban rashi ne. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu, ya ba iyalansu hakuri da juriyar rashin.

Sakatariyar kungiyar, Kwamarad Bilkisu T. . ta kuma bukaci al’umma da su rinka sanya matasa cikin addu’a tare da ba su shawarwari masu kyau a duk inda aka tsinci kansu.

Kungiyar ÀoPSHoN ta mika sakon ta’aziyya ta musamman ga dangin wadanda suka rasa rayukansu, tana mai addu’ar Allah ya ba su hakuri da dangana, ya kuma sa su huta lafiya a gidan gaskiya.

A karshe, kungiyar ta bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da hada kai da nuna jinkai a wannan lokaci mai cike da alhini da jimami, domin cigaban jihar da jin dadin al’umma baki daya.


Comments

Popular posts from this blog

AoPSHoN Commends SUBEB Chairman Kabir’s Tireless Efforts, Celebrates National Award Recognition

NASU Hails SUBEB Chairman Yusuf Kabir for Exemplary Service, Applauds National Labour Award

RASHIN DA YA GIRGIZA KANO: NASU TA MIKA TA’AZIYYA KAN HATSARIN MATASA 22