RASHIN DA YA GIRGIZA KANO: NASU TA MIKA TA’AZIYYA KAN HATSARIN MATASA 22
Daga JB Danlami
Jihar Kano ta tsinci kanta cikin yanayi na alhini da jimami sakamakon wani hatsarin mota mai muni da ya yi sanadiyyar mutuwar matasa 22 ‘yan asalin jihar Kano Wannan hatsari da ya auku a lokacin dawowar su daga Abekuta babban birnini jihar Ogun bayan kammala gasar wasanni. Ta kasa
Kungiyar Ma’aikatan SUBEB wadanda ba malamai ba, wato NASU, ta nuna alhininta da sakon ta’aziyya cikin kalmomi masu sanyi da tausayi. A cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Kwamarad Aminu Ali Maikudl, ya fitar, ya bayyana cewa wannan lamari rashi ne da ba za a manta da shi cikin gaggawa ba.
Lamarin da ya faru ba kawai ya shafi iyalan marigayan ba, har ma da alummar jihar Kano da Kasa baki daya. "
"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya karbi rayukansu cikin rahama,” in ji Kwamarad Aminu.
Kwamarad Aminu ya kuma mika sakon ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, yana mai bayyana cewa wannan ibtila’i ya shafi kowa da kowa.
A karshe, kungiyar NASU ta yi addu’ar Allah ya jikan matasan da suka rasu, ya kuma bai wa iyalansu da al’ummar jihar Kano hakurin jure wannan babban rashin
Comments
Post a Comment