Ziyarar duba makarantu
Mun yi shiri tsaf na kai ziyara makarantu a sabon zangon karatu: Dr. Hayyo
Daga Jb Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Dr. Danlami Hayyo, yace Hukumarsa ta yi shiri tsaf na kai ziyara makarantu, a sabon Zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2022 zuwa 2023.
Dr. Hayyo, ya bayyana haka cikin sakonsa na shiga sabuwar shekara ga daukacin alummar jihar nan, ta bakin mai Magana da yawun hukumumar Balarabe Danlamai Jazuli.
Shugaban Hukumar, ya kara da cewa, bisa al’ada Hukumar na tsara kai ziyara ga makarantu tun daga ranar da aka koma, domin tabbatar da cewa, malamai da dalibai sun koma bakin aiki kamar yadda aka tsara.
Ya tunatar da shugabannin makarantu cewa, babu wata rana da aka ware a makon farko da komawa makarantu wadda ba za’a yiwa dalaibai kataru ba.“Jami’anmu a matakin jiha, da shiyyoyin ilimi da matakan Kananan Hukumomi zasu kai ziyara makatanu a ranar da aka koma, don haka nake gargadin malamai da cewa, su tsara darrusan karatu, kuma su shiga ajujuwa, su koyar, yin haka shi ne doka ta tsara” inji Dr. Hayyo
Da ya juya ga bangaren iyayen yara kuwa, Dr Hayyo ya hore su, da su tura ‘yayansu makaranatu da zarar an koma, in da ya kara da cewa, sai iyaye sun bayar da goyon baya ga tsare –tsaren ilimin sannan za’a iya kai wa ga nasara
Ya yi amfani da wannan dama, wajen taya Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusif Gawuna da daukacin manyan da kananan jami’an Gwamnati, murnar shigowa sabuwar shekarar miladiya ta 2023
Har ila yau, shugaban Hukumar ta ilimin Bai Daya, ya aike da makamancin wannan sakon ga saraku nan jiha da malaman addini, tare da yin musu fatan alheri a cikin wannan shekara da sauran shekaru masu zuwa.
wasu daga cikin ayyukan SUBEB
Comments
Post a Comment