Posts

Showing posts from September, 2024

Kwamishinan Ilimi na Jiha ya Kai ziyarar aiki a KH Tsanyawa

Daga Tsanyawa   Kwamishinan Ilimi na Jiha, Hon.  Umar  Huruna  Doguwa  ya kai  ziyarar   aiki a  KH  Tsanyawa. Da yake jawabi kwamishinan ya ce, ziyarar tasa  ta biyo bayan ziyarar ba zata da Gwamna Abba Kabir Yusif, ya kai a wasu Makarantun yankin bayan dawowarsa  daga jihar Katsaina. Ya kara da cewa, Gwamnan ya nuna jindadi matuka bisa tarar da Shugabanin makaratun a bakin aiki duk kuwa da  cewa, ana cikin hutun karshen zango na uku a daukacin Makarantun Jihar nan. Hon Haruna, ya bayyana gamsuwar Gwamna Abba  bisa  kokarin wadannan Shugabannin Makarantun, inda ya bayar da umarnin daga  darajarsu da kuma gyara Makarantun da suke shugabanta.  Kwamishinan ya ce, Gwamnan ya ba da umarnin kewaye Makarantar Tsanyawa Model  da haka famfon tuka -tuka a wannan  makarantar. Kazalika, Kwamishinan  ya ziyarci  Makarantun Firamare ta Tsanyawa da 'Yankamaye da Riyadul Kur'an da Kabagiwa sai...