Kwamishinan Ilimi na Jiha ya Kai ziyarar aiki a KH Tsanyawa

Daga Tsanyawa 

 Kwamishinan Ilimi na Jiha, Hon.  Umar  Huruna  Doguwa  ya kai  ziyarar   aiki a  KH  Tsanyawa.

Da yake jawabi kwamishinan ya ce, ziyarar tasa  ta biyo bayan ziyarar ba zata da Gwamna Abba Kabir Yusif, ya kai a wasu Makarantun yankin bayan dawowarsa  daga jihar Katsaina.

Ya kara da cewa, Gwamnan ya nuna jindadi matuka bisa tarar da Shugabanin makaratun a bakin aiki duk kuwa da  cewa, ana cikin hutun karshen zango na uku a daukacin Makarantun Jihar nan.

Hon Haruna, ya bayyana gamsuwar Gwamna Abba  bisa  kokarin wadannan Shugabannin Makarantun, inda ya bayar da umarnin daga  darajarsu da kuma gyara Makarantun da suke shugabanta.

 Kwamishinan ya ce, Gwamnan ya ba da umarnin kewaye Makarantar Tsanyawa Model  da haka famfon tuka -tuka a wannan  makarantar.

Kazalika, Kwamishinan  ya ziyarci  Makarantun Firamare ta Tsanyawa da 'Yankamaye da Riyadul Kur'an da Kabagiwa sai Kuma makaratar Firamare ta garin  'Yargwanda, inda ya bukaci Shugabannin Makarantun da Malamansu su ci gaba da zage damtsen wajen gudanar da ayyukansu 

Sakataren Ilimin yankin Kwamared Sule A. Haruna,  ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusif bisa cika alkawarin da ya yi na daga likkafar Shugabannin Makarantun da ya samu a bakin aiki a lokacin hutu.

Kazalika, ya yabawa kwamishinan Ilimi na Jiha bisa yadda yake Kai kawo wajen sauya fasalin harkokin Ilimi a Jihar nan.

Sakataren Ilimin, ya yi amfani da wannan dama ya jaddada aniyarsa wajen ci gaba da yi wa Shugabannin Makarantun jagoranci don kara inganta harkar Ilimi a yankin.

Wakilinmu na yakin Sani Lawan Tsanyawa ya ba mu labarin cewa alummar yakin sun nuna godiyarsu bisa wannan ziyara ta kwamishinan Ilimi.

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!