Kwamishinan Ilimi na Jiha ya Kai ziyarar aiki a KH Tsanyawa
Daga Tsanyawa Kwamishinan Ilimi na Jiha, Hon. Umar Huruna Doguwa ya kai ziyarar aiki a KH Tsanyawa. Da yake jawabi kwamishinan ya ce, ziyarar tasa ta biyo bayan ziyarar ba zata da Gwamna Abba Kabir Yusif, ya kai a wasu Makarantun yankin bayan dawowarsa daga jihar Katsaina. Ya kara da cewa, Gwamnan ya nuna jindadi matuka bisa tarar da Shugabanin makaratun a bakin aiki duk kuwa da cewa, ana cikin hutun karshen zango na uku a daukacin Makarantun Jihar nan. Hon Haruna, ya bayyana gamsuwar Gwamna Abba bisa kokarin wadannan Shugabannin Makarantun, inda ya bayar da umarnin daga darajarsu da kuma gyara Makarantun da suke shugabanta. Kwamishinan ya ce, Gwamnan ya ba da umarnin kewaye Makarantar Tsanyawa Model da haka famfon tuka -tuka a wannan makarantar. Kazalika, Kwamishinan ya ziyarci Makarantun Firamare ta Tsanyawa da 'Yankamaye da Riyadul Kur'an da Kabagiwa sai...