Zan yi koyi da shugabanci irin na Dr. Danlami Hayyo: ES Dala Daga Balarabe Danlami Jazuli Sakatariyar Ilimin Karamar Hukumar Dala, Hajiya Halima Mustafa, ta ce zata yi koyi da irin tsarin jagoranci na shugaban Hukumar Ilimi na Jiha Dr. Danlami Hayyo, bisa yadda yake bijiro da ayyuka da suke da nufin daga darajar ilimi a fadin jihar nan. Hajiya Halima, ta furta hakan ne, a lokacin da ta kai ziyarar aiki sashen Hulda Jama’a na Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha, dake sakatariyar Audu Bako a nan babban birnin jiha. Sakatariyar Ilimin ta ci gaba da cewa, a matsayinsu na wakilan Hukumar Ilimin Bai Daya a matakin karamar Hukuma nauyi ne da ke kansu, na tabbatar da cewa dukkanin malamai da sauran maaikata da suke karkashinsu suna yin aikin da yakamata a lokacin da ya dace, don cin halalin abin da gwamnati take biyansu. Ta kara da cewa, da zarar an koma makarantu bayan kammala hutu, ita da sauran manyan...