Hukumar Ilimin Bal Daya ta kasa ta horar da jamian Hulda da Jama'a na Jihohi 36 da Abuja

Daga Usman Da’u Isah 

A dai dai lokacin da aka kammala taron bita na kwanaki hudu ga jamian Hulda da jama’a na  Hukumomin Ilmin Bai Daya jihohin kasar nan talatin da shida hade da birnin tarayya Abuja, wanda ya gudana a jihar Bauchi, an karrama wasu daga cikin Jamian Hulda da jama’a na wasu  jihohi.

Da yake jawabi a wurin taron bitar, shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya Ta kasa, Dr. Hamid Bobboy, wanda ya samu wakilcin daraktan shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan, Mallam  Abdussalam  Abubakar ya ce, duniya ta samu sauye-sauyen  fasaha, wanda ya zama wajibi ga Jamian Hulda da jama’a, su kara tashi tsaye don fuskantar kalubalen zamani ta fuskar yada labarai.
Dr. Hamid Bobboy,  ya bukaci mahalarta taron su tabbatar da tattauna abubuwa da zasu habaka harkar yada labarai don sanar da alumma irin kokarin da Hukumar take yi,  wajen  samar da ilimi Bai Daya ga daliban kasar nan.

A lokacin taron bitar an gabatar da Makalu
 da kasidu tare da kai ziyara  wasu muhimman wurare, kazalika an raba takardun yabo ga wasu jamian hulda da jama’a bisa kokarinsu na yada labaran ayyukan Hukumar a matakin kasa da jihohhinsu.

Da yake karbar takardar karramawa, 
Balarabe Danlami Jazuli, jami’in Hulda da jama’a na jikar Kano, ya taallaka nasarorin da sashen ke samu da yadda shugaban Hukumar na jihar Kano Dr. Danlami Hayyo yake bai wa sashen kulawa da ta kamata ta hanya samar da kayan aiki, horar da maaikata, har ila yau da inganta walwala da jindadin manya da kananan maaikatan sashen.
Ya kuma yi amfani da wannan lokaci ya godewa shugaban bisa daukar nauyin halartarsa zuwa wajen wannan taro.  

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!