An kammala taron bita kan dabarun koyarwa na RANA


Daga Balarabe Danlami Jazuli

Hukumar Ilimin Bai Daya ta kasa (UBEC) da Hadin Gwiwar Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha (SUBEB) da tallafin Bankin dunuiya karkashin (BESDA) sun shirya taron bita ga manyan jami’an bayar da horo kan shirin koyar karatu da rubutu da lissafi mai taken (RANA)

 Da yake jawabi ga mahalarta taron bitar a otel din Three Star dake birnin Dutseb Jihar Jigawa, Shugaban Hukumar Ilimin na Jiha,  iDr, Danlami Hayyo ya ce an shirya taron bitar ne don kara kaifafa  fahimatar dabarun koyarwa na shirin RANA ga jamian da zasu kayar da malaman makaranta a matakan kananan Hukumomi. 
Dr, Danlami Hayyo wanda ya samu wakilcin Kwamishina na daya, Alhaji Kabiru Ahmad , yace manufar wanan taron bita ita ce, don kara horar da manyan jami’an  da zasu horar da malaman da
makaranta, kan dabarun Koyar da daliban firamare karatu da rubutu da lissafi cikin sauki, inda ya kara da cewa, shirin  ya tanadi koyar da dalibai cikin harshen Hausa domin samun saukin fahimta 
Bugu da kari, shugaban hukumar yace, dabarun koyarwa na RANA an tsara su ta hanyar koyarwa cikin nishadi, wanda suka kunshi wakoki da wasanni domin jan hankalin dalibai su mayar da hankali ga darrussan da ake koya musu.

Dr. Hayyo,  ya yi amfani da wannan dama, ya bukaci iyaye da daukacin alaumma, su ci gaba da bayar da gudummawar da takamata, wajen tallafawa kokarin gwamnati kan inganta fannin ilimi a jihar nan. Kazalika,ya zayyana  wasu daga cikin nasarori da aka samu a shirin RANA Karkashin shirin BESDA wadanda suka hada da koyar da dalibai karatu da rubutu da lissafi. 

Har ila yau, Dr. Hayyo  ya godewa kokarin gwamnatin jiha, karkashin jagorancin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa yadda yake iya bakin kokari na bunkasa ilimi a matakin farko. 

A jawabansu daban daban, daraktan lura da makarantu  Alhaji Almu Musa Baba da takwaransa mai kula da tabbatar da ingantuwar ayyuka, Mallam Mustafa Madaki  Huguma, sun hori mahalarta taron bitar da su su ci gaba da bayar da hadin kai ga malaman bitar domin samun nasarar shirin a dukkanin matakai.

 Shi ma da yake jawabi, Daraktan Horar da malamai malam Yakubu Muhammad ya bayyana  cewa, shirin BESDA wanda yake samun tallafi daga Bankin Duniya shiri ne da yake  da manufar dawo da yara da ba sa zuwa makaranta su koma zuwa makaranta domin a bunkasa iliminsu.
Wasu daga cikin mahalarta taron bitar Dr. Hannatu Ado Ahmad and Mallam Bashir Indabo sun godewa shugaban Hukumar Ilimin Bai adaya Dr. Danlami Hayyo bisa jajircewasa wajen ganin an samu nasara shirin. 

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!