Daga Dala LGEA, Kano
Zan yi koyi da shugabanci irin na Dr.
Danlami Hayyo: ES Dala
Daga Balarabe Danlami Jazuli
Sakatariyar Ilimin Karamar Hukumar Dala, Hajiya Halima Mustafa, ta ce zata yi koyi da irin tsarin jagoranci na shugaban Hukumar Ilimi na Jiha Dr. Danlami Hayyo, bisa yadda yake bijiro da ayyuka da suke da nufin daga darajar ilimi a fadin jihar nan.
Hajiya Halima, ta furta hakan ne, a lokacin da ta kai ziyarar aiki sashen Hulda Jama’a na Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha, dake sakatariyar Audu Bako a nan babban birnin jiha.
Sakatariyar Ilimin ta ci gaba da cewa, a matsayinsu na wakilan Hukumar Ilimin Bai Daya a matakin karamar Hukuma nauyi ne da ke kansu, na tabbatar da cewa dukkanin malamai da sauran maaikata da suke karkashinsu suna yin aikin da yakamata a lokacin da ya dace, don cin halalin abin da gwamnati take biyansu.
Ta kara da cewa, da zarar an koma makarantu bayan kammala hutu, ita da sauran manyan jami’an sashen ilimin yankin, zasu gudanar da aikin kai zaiyara makarantu, domin tabbatar da cewa dukkanin malamai da aka tura suna zuwa aiki kan lokaci, inda ta gargadi masu wasa da aiki da su kuka da kansu, domin kuwa hukuncin dokar aiki na nan na jiran masu nuna halin ko in kula da ayyukansu.
Kazalika Hajiya Halima ta yi alwashin karrama duk malaman da suke aiki bil hakki da gaskiya a wani mataki na karfafa musu gwiwa.
Sakatariyar Ilimin ta yi amfani da wannan dama ta godewa shugaban Hukumar Ilimi na Jiha, Dr. Danlami Hayyo bisa yadda a koda yaushe yake karfafawa sakatarorin ilimi gwiwa, kan su ci gaba da jajircewa wajen aikinsu, don samun nasarar bunkasa ilimi a yankunansu.
Har ilayau, Hajiya Halima ta godewa, shugaban Karamar Hukumar Dala, Alhaji Ibrahim Sulaima Dan Isle da ‘ Yan majalisarsa bisa yadda suke iya bakin kokari na magance matsalolin ilimin yankin.
Comments
Post a Comment