Rimin Gado LGEA
Mun tsara jadawalin ziyarar makarantu da zarar an koma : Sakataren Ilimin KH Rimin gado
Daga Jb Danlami
Sakataren Ilimin Karamar Hukuamar Rimin Gado, Malam Nasiru
Haladu ya ce sashen Ilimi Karamar Hukumar ya yi tsare- tsare na kai ziyara
makarantu a makon farko na zagon Karatu na biyu na shekarar karatu 2022 zuwa
2023.
Bayaninin haka ya fito ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa
hannu jami’in wayar da kai na sashen ilimin yankin (Social Mobilization) Malam
Alhasan Hassan Abba wadda ya turo ga
sashen Hulda da jama’a da yada labarai na
Hukamar Ilimin Bai Daya ta Jiha.
Malam Nasiru, ya kara da cewa, daya daga cikin muhimman ayyuka na sashen ilimi a matakan kananan Hukumomi shi ne, bibiya domin tabbatar da cewa ana gudanar da ayyukan koyarwa bisa ka’idojin da hukumar ilimin Bai daya ta yi tanadi.
Ya sanar da cewa, baya ga jami’an sashen Ilimi na yankin, sauran jami’ai a matakin shiyyar
ilimi da babbar shelkwatar Ilimin Bai Daya ta jiha zasu kawo ziyara a makarantun yankin, domin duba yadda
malamai da dalaibai suka koma bakin aiki bayan kammala hutun zangon farko.
Sakataren ilimin, ya
ja kunnne malamai da su tabbata sun daura damara, ta fara aiki daga ranar da
aka koma, domin kada a kama su da laifin sakaci da aiki.
“Duk malaman da aka
samu da laifin sakaci da aiki, hukuncin da
ya biyo baya su suka jawa kansu ” cewar sakataren ilimin
kazalika, ya bukaci iyaye da su tabbata suna tura ‘ya’yansu
makaranta domin su ci gaba da cin moriyar tsatre- tsaren ilimi na Gwamantin Dr. Abdullahi Umar Ganduje
A cikin sanarwar sakateren ilimin, ya godewa Shugaban Hukumar
Ilimin Bai Daya na jiha, Dr Danalmi Hayyo, bisa yadda yake dora su kan gwadaben da
ya dace na lura da ayyuka, wanda yake cewa hakan ne ta ke kara zaburar da su
kan ayyukansu.
Har ila yau, ya yi godiya ga Shugaban Karamar Hukumar ta Rimin Gado Barrista Dahiru Maigari bisa gudummawarsa ga sashen ilimin yankin.
......,.................................................
Comments
Post a Comment