Daga Rimin Gado LGEA

MUN SHIRYA TSAF DON TUNKARAR ZANGON KARATU NA BIYU 

Daga SMO Alahasan Hassan Abba

A shirye – shiryen komawa makarantu daga hutun zangon karatu na farko shekarar 2020/2023 sakataren ilimi na karamar hukumar Rimin Gado Mallam Nasiru Haladu,  ya gana da jamian duba makarantu  da masu kula da ingancin koyo da koyarwa na karamar hukmar, domin zaburar da su kan tunkarar zango karatu na biyu.

Da yake jawabi a gurin wani taro da manyan jami'an. Malam bNasiru ya hore su da su jajirce wajen gudanar da aiyukansu na duba makarantu da malamai da ke karkashinsu don tabbatar da cewa kowanne shugaban makaranta da malaman sa sun dawo bakin aiki cikin shiri da gabatar da aiyukansu na koyo da koyarwa.daga randa aka koma, domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ya kara da cewa Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje  ta hannu  Shugaban SUBEB Dr. Dallami Hayyo na kokari wajen habbaka ilimi, musaman na firamare da karamar sakandare da babba, da kuma kula da hakkokin malamai wajen  biyansu albashi akan lokaci. 

Sakataren ilimin ya nanata cewa ba zai laminci sakaci da aiki ba, da kin zuwa aiki ko makara ba tare da muhimmin uzuri ba
.
 Ya kuma kara jan kunnen  malamai da lallai su tabbatar kowanne malami ya shirya tsaf don gudanar da aiki daga ran da aka koma makaranta tare da gabatar da aiki ga yara domin a yanzu ba wani batun satin share – share ..

Malam Masiru ya kuma furta  cewaduk wanda aka samu da sakaci da aiki hukuma ba za tai kasa a guiwa ba wajen hukunta shi 
.A karshe ya tabbatar da cewa tuni an tsara jadawalin ziyarar makarantu da zarar an koma makaranta, domin a wannan zango karatun  ba zama a ofis a jira rahoto , don haka za a fita zagayen makarantu gaba daya da dukkan shuwagabannin sashi – sashi  na maaikatar ilimi na wannan karamar hukuma .

.....,..............................,......,..,.,............

Dr. Danlami Hayyo a Gidan Rediyon Express

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!