Gobara ta kone ajujuwa a wata makaranta a Garun Malam
Daga Jb Danlami
Wata gobora da ba’a san dalilin tashin ta ba, ta yi sanadiyar konewar wasu ajujuwa biyu tare da ofishin shugaban makarantar Iyya’udden Islamiyya dake Garun Mallam a yankin Karamar Hukumar Garun Malam.
Sakataren Ilimin Yankin, Mallam Sani Mato, ya sanar da hakan ga sashen Hulda da jama’a na Hukumar Ilimin ta Jiha ta hannun shugaban sashen wayar da kai na sashen ilimin yankin Malam Yusif Garba.
Malam Sani, ya kara da cewa, koda dai al’amarin gobarar ya faru cikin tsakiyar dare, amma ana kyautata tsammanin cewa, tashin wutar na da alaka da ayyukan wasu bata gari.
Ya kara da cewa, alumma na da rawar takawa wajen kare duk wasu gine- ginen mallakin alumma ,domin hana marasa kishi lalatawa da gangan.
Sakataren Ilimin, ya kuma bayyana cewa zasu dauki mataki na sanar da Hukumomi da suka dace don daukar mataki cikin hanzari
“Zamu nemi goyon bayan ofishin Hisba da na Bijilanti da sauran jami’an tsaro da masu unguwanni don samar da tsaro a makarantunmu” cewar sakataren ilimin
Bugu da kari, Malam Sani mato, ya nemi agajin shugaban Hukumar Ilimin Bai Day
na jiha. Dr. Danlami Hayyo da shugaban Karamar Hukumar ta Garun Malam Hon, Mudassiru Aliyu Dakasoye kan kawo wa makaranatar daukin gaggawa.
,,...,.,.................................................
Comments
Post a Comment