Ilimi-Gidan Makama

Mun gamsu da zuwan dalibai makaranta-Shugabar Makarantar Firamare ta Gidan Makama Daga 
Jb Danlami

Shugabar makarantar firamare ta Gidan Makama a yankin Karamar Hukumar Birni,  Hajiya Sadiya Tahir,  ta yabawa iyayen daliban Makaranatar , bisa yadda suka tura ‘yayansu makarantar  kan kari, a ranar farko da aka bude makarantar.

Hajiya Sadiya, ta furta haka a lokacin zantawarta da sashen yada labarai na Hukumar ta Ilimi Bai Daya ta Jiha.Shugabar makarantar, ta ce alamu sun nuna cewa, dalibai da iyayensu sun zaku da a bude makarantu,  wanda hakan ce ta sanya daliban suka yi tururuwar zuwa makaranta da sanyin safiyar da aka bude makarantu.

“A ranar da muka koma makaranata, duk da cewa ana cikin yanayin sanyi amma dalibai sun hallara kan lokaci”. In ji Hajiya Sadiya Tahir

Ta yi amfani da wannan dama ta gedewa iyayen yara, bisa amsa kiran da aka yi musu na cewa, su tura yaransu makarantu da zarar an bude.

Kazalika, ta godewa Shugaban Hukumar Ilimin Bai daya na Jiha, Dr. Danlami Hayyo, bisa yadda ya zaburar da Shugabannin  makarantu da malamai da iyayensu kan muhimmancin komawa makarantu kan kari.

“Mun gamsu da zuwan dalibai haka ce ta sanya muka umarci malamai su shiga aji kuma su aiwatar da darrussa” In ji shugabar makarantar

Har ila yau, ta godewa malamanta bisa bin umarnin Hukumar Ilimin Bai daya ta Jiha, inda suka koma bakin aiki kan lokaci. 

Makarantar Firamare ta Gidan Makama 

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!