Daga Ungogo

Mun gamsu matuqa da gudummawar Dr. Danlami Hayyo ga ci gaban ilimi a yankinmu- Hakimin Ungogo

.Daga JB Danlami

Hakimin Ungogo, Magajin Malam, Alhaji Ahmad Abduqadir Chedi, ya bayyana cewa, alummar  yankin ba su taba samun ayyuka da suka bunqasa ilimi ba, sai da dansu Dr. Danlami Hayyo ya samu shugabancin Hukumar ilimin Bai Daya ta jiha.

Alhaji Ahmad Chedi,  ya furta hakan a lokacin bikin bude wasu makarantun Firamare biyu a Garin   Ungogo da ta Garin Rangaza wadanda aka daga matsayinsu zuwa makarantu Gwaji (Model Schools) .

Hakimin, wanda ya samu wakilcin, Alhaji Shehu Ahmad Abduqadir Chedi, ya qara da cewa, a matsayinsu na iyayen alumma, ya zama wajibi su yabawa duk wanda ya aiwatar da ayyukan ci gaba ga alummarsu.

Sai ya hori daukacin shugabannin alumma, a yankin,  su dinga nusar da jama’arsu muhimmancin alkinta kayayyaki da hukuma ta samar don ci gaba. 
Kana ya umarci iyayen yara, su dinga sanya ‘ya ‘yansu a makaranta don cin gajiyar ayyukan ilimi da aka samar musu..

 A jawabansu daban-daban, Shugabannin Kwamitocin  Alumma Gatan Makaranta (SBMC)  na Makarantun biyu wato Makarantun Gwaji  na garuruwan Ungogo da Garin Rangaza Malam Balarabe Shuaibu da Alhaji Isah Haruna, sun ce sun shirya taron ne don nuna Godiya matuqa ga Dr. Danlami Hayyo wajen daga likkafar makarantun nasu biyu, inda suka yi alqawarin ci gaba da bayar da gudummawa da ta kamata don ci gaba da daga darajar ilimi a makarantu. 

Su ma da suke bayani shugabannin Qungiyoyin Iyaye da Malaman Makaranta (PTA)  Mallam Haruna Sale da Alhaji Kabiru Dabo,  sun ce ba zasu taba  mantawa da irin gudummawa da Dr. Danlami Hayyo ya yi musu ba, wajen daga likkafar makarantun garuruwan nasu.

A jawabinsa na maraba Sakataren Ilimin yankin, Mallam Muhammad Yahaya,  ya ce ayyukan raya ilimi da yankin ya amfana sun hadar da gina sabbin makarantu da gyaran wasu da dama, har ila yau, da gina katafariyar makarantar zamani a garin Tarda.

Sakataren Ilimi, ya yi alwashin yi wa makarantu biyu jagoranci don su ci gaba da rike kambu na zamowa makarantu abin misali ba a yankin kawai ba, har da jiha baki daya.

Shugaban Hukumar Ilimn Bai daya na jiha, Dr. Danlami Hayyo  yace nan gaba ne alummar yankin zasu fahimci irin ayyukan alheri da suka mora kasancewarsa dan asalin yakin, kuma ya samu dama ta hidimtawa alumma da jiha baki daya.

Ya godewa wadanda suka shirya taron tare da nanata kudurinsa na ci gaba da ba da gudummawa ta kashin kansa  don tallafawa ilimi a yankin,

Wakilinmu Usamn Da’u isah da ya halarci taron ya bayyana mana cewa jama’a da dama sun halarci taron.

Comments

Popular posts from this blog

Newly recruited BESDA Teachers In Tarauni LGEA receives letters of appointment

Bichi LGEA Distributes BESDA Offer of Appointment to Newly Recruited Facilitators

Announcement! Announcement!! Announcement!!!